Shugaba Obama ya bude shafin Twitter

Hakkin mallakar hoto TWITTER
Image caption Shafin wata dama ce ga Amurkawa da za su rika bayyana wa Shugaban abin da ya dame su

Shugaba Obama ya bude shafin Twitter kamar yadda fadar gwamnatin Amurkan ta White House ta tabbatar.

Shafin mai adireshin @POTUS (President Of The United States), cikin minti 24 da bude shi ya samu mabiya 100,000.

A sakon shugaban na farko a shafin, ya rubuta, ''Hallo, Twitter! Barack ne. Kwarai hakika ! Bayan shekara shida, a karshe dai sun ba ni shafina.''

Shafin Twitter na Shugaban na hukuma yana da mabiya miliyan 59 da 300,000.

An bude shafin ne mai adireshin @BarackObama, a shekara ta 2007, kuma rubutunsa na farko a lokacin ya fara ne da harufan BO.

Sabon shafin Twitter din na @POTUS, zai kasance wata sabuwr hanya da Shugaba Obaman zai rika mu'amulla kai tsaye da Amurkawa.

Zai rika rubuta sako da bayanai da kansa ne inji sanarwar da fadar gwamnatin ta bayar.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Shugaban ya kuduri aniyar mayar da gwamnatinsa ta kasance mafi saurare da mu'amulla da jama'a a tarihi.

Kuma shafin na @POTUS zai bai wa Amurkawa sabuwar hanyar bayyana ra'ayinsu kan abubuwan da suka fi damun su.

A yanzu dai Shugaba Obama yana bin mutane 65 da suka hada da Bill Clinton da George Bush da kuma shafin @FLOTUS na matarsa(na hukuma).

Sai dai ba ya bin Hillary Clinton ko Fira ministan Biritaniya David Cameron.

Tsohon Paparoma Benedict na 16 ya samu mabiya 280,000 a shafinsa na Twitter na Ingilishi a ranar frko da ya bude shi a watan Disamba na 2012.

Yanzu kuma shafin, wanda Paparoma Francis ke amfani da shi, yana da mabiya miliyan shida da 100,000.