PDP ta rufe shafinta na Facebook da Twitter

Hakkin mallakar hoto muazu facebook
Image caption Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Alhaji Ahmed Adamu Mu'azu

Jam'iyyar PDP a Nigeria ta sanar da rufe shafukanta na Facebook, da Twitter saboda abin da ta kira kutsen da wasu suka yi mata a shafukan.

Kakakin jam'iyyar PDP, Oliseh Metuh, a cikin wata sanarwa, ya ce hakan ya biyo bayan yadda ake fitar da sanawar daga shafin wadanda ba uwar jam'iyyar ce ta wallafa da kanta ba.

A karshen wannan makon ne aka wallafa a shafukan na zumunta na jam'iyyar PDP cewar jam'iyyar ta dauki alhakin duk kura-kuran da ta yi cikin shekaru 16 da ta yi tana mulkin Nigeria.

Sanarwar ta ce jam'iyyar za ta ci gaba da aiki domin sake fasali na tunkarar zaben 2019.

Daga karshe, jam'iyyar ta PDP ta bukaci kafafen yada labarai su tantance labaransu da kyau kafin su wallafa abubuwan da suka shafe ta.