Dan kunar bakin wake ya kai hari a Adamawa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kwana biyu ba a ji sako daga wajen Abubakar Shekau ba

Rahotanni daga jihar Adamawa na cewa wani dan kunar bakin wake ya kai hari a wata kasuwar dabbobi a garin Garkida da ke karamar hukumar Gombi.

Shaidu sun ce akalla mutane bakwai suka rasa rayukansu wasu hudu suka jikkata.

Bayanai na cewa maharin ya tayar da bam din ne da misalin karfe daya da kwata, a daidai wurin binciken masu shiga kasuwar ta dabbobi.

'Yan Boko Haram sun sha kai hare-haren kunar bakin wake a sassa da dama a yankin arewa maso gabashin Nigeria.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwa dubban mutane da kuma raba wasu fiye da miliyan uku da muhallansu.