Harin Bom ya kashe mutane 4 a birnin Kabul

Harin bam a birnin Kabul Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Harin bam a birnin Kabul

Mutane hudu ne suka hallaka yayinda da dama suka samu raunuka a wani harin kunar bakin wake a Kabul babban birnin kasar Afghanistan

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Afghanistan din ta tabbatar da abkuwar lamarin.

Kungiyar Taliban dai ta yi ikirarin kai harin, wanda aka kai kusa da filin ajiyar motoci a Ma'aikatar Shari'ar kasar, a daidai lokacin da ma'aikata ke ribibin komawa gida.

Dama dai mayakan Taliban sun saba kaddamar da hari a wuraren cunkosun jama'a.

A ranar Alhamis da ta gabata ne mayakan na Taliban din suka kai hare-hare a wani gidan saukar baki, inda mutane 14 suka rasa rayukansu, ciki har da 'yan kasashen waje tara.