Dubban mutane na tserewa daga Ramadi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutane na tserewa daga garin Ramadi

Dubun dubatan fararen hula a Iraki suna tserewa daga birnin Ramadi, a daidai lokacin da mayakan kungiyar IS ke ci gaba da iko a birnin.

Majalisar dinkin duniya ta ce mutane dubu 25 sun fice daga birnin a cikin 'yan kwanaki, sun kama hanyar zuwa birnin Bagadaza.

Mutane fiye da 130,000 ne suka fice daga birnin Ramadi a cikin wata guda tun bayan da mayakan IS suka shiga cikin birnin.

Kungiyoyin agaji sun soma ba da tallafin abinci da ruwa da kuma magunguna a wasu sansanonin wucin gadi.

A yanzu haka mayakan sa-kai 'yan Shi'a da ke samun goyon bayan Iran na kan hanyarsu ta zuwa Ramadi a kokarin fafata da mayakan IS.

Wakilin BBC a gabas ta tsakiya ya ce komawar birnin Ramadi hannun 'yan Shi'a babban kalubale ne ga gwamnatin Iraki.