Gobara ta lalata wani yankin kasuwar Katsina

Image caption Gobarar da ta lalata kasuwar Sokoto

Gobarar da ta tashi a cikin dare a babbar kasuwar Katsina ta kona wasu shaguna inda aka yi hasarar dukiya mai yawa.

Gobarar ta shafi rukunin wasu shaguna ne da ke yankin da ake kira na wucin-gadi.

Bayanai sun ce abubuwan da gobarar ta lalata sun hada da gwala-gwalai, da tufafi da kuma wayoyin salula da miliyoyin naira.

Rahotanni sun ce wutar ta yi kusan awa uku tana ci kafin a kashe ta.

Ko a shekara ta 2012 ma sai da gobara ta tashi a wannan yankin a kasuwar.