Kerry zai halarci bukin rantsar da Buhari

Hakkin mallakar hoto Buhari Campaign
Image caption Mr Kerry a lokacin da ya ziyarci Buhari kafin a gunadar da zabe

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ne zai jagoranci tawagar Amurka a bukin rantsar da zababben shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari a mako mai zuwa.

Sanarwa daga fadar White House ta ce za a sanar da sunayen sauran 'yan tawagar a cikin kwanaki masu zuwa.

A ranar 29 ga watan Mayu za a rantsar Buhari, bayan ya samu galaba a kan shugaba Goodluck Jonathan a zaben da aka yi a watan Maris a fadin kasar.

Ana sa ran, shugabannin kasashe daga sassa daban-daban na duniya za su halarci bukin wanda za a yi a Abuja.

Zaben da aka yi a Nigeria na cike da tarihi, inda jam'iyyar adawa ta lashe a karon farko tun bayan da kasar ta koma bin tsarin demokuradiyya a shekarar 1999.