Gwamnonin Nigeria sun zabi sabon shugaba

Hakkin mallakar hoto zamfara website
Image caption Gwamna Yari ya zama shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya

An bayyana gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari a matsayin sabon shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya a karshen taron kungiyar a babban birnin kasar, Abuja.

Shugaban kungiyar mai-barin-gado, kuma gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi wanda kuma shi ya karanta bayanin bayan taro, ya ce an zabi Abdul'aziz Yari ba tare da wata adawa ba.

Shi dai Yari ya kasance mataimakin shugaban kungiyar a baya. To sai dai kuma ba a zabi sabon mataimakinsa a wajen taron ba.

Kungiyar dai ta fada cikin rikicin shugabanci a watan Mayun 2013 bayan zaben shugabanta, a inda ta rabu gida biyu wato bangaren Rotimi Amachi da na Jonah Jang, gwamnan jihar Plateau.