'Yan sanda 11 za su gidan yari

Image caption Kotu a Afghnistan

Wata kotu a Afganistan ta yanke wa wasu 'yan sanda 11 hukuncin shekara daya a gidan yari sakamakon rashin kare wata mata daga dukan da zauna gari banza suka yi mata wanda yayi sanadiyar mutuwarta a watan Maris din da ya gabata.

An saki 'yan sanda takwas daga cikin wadanda aka tuhuma da laifin sakamakon rashin shaida da ke nuna hannunsu a cikin sakacin.

An kai wa matar mai suna Farkhunda harin ne a wani wurin bauta, bayan an zarge ta da kona Al-qura'ani mai girma.

Mutane sun yi Allah-wadai da hukuncin da kotu ta yanke, inda wani dan majalisar dokoki na kasar ya ce kamata ya yi a tsare shugaban 'yan sandan Kabul.

Tuni dai aka yanke wa mutane hudu hukuncin daurin rai da rai sakamakon hannu da suke da shi a kisan Farkhunda.

An kuma yankewa wasu mutane takwas din daban hukuncin shekaru 16 a gidan yari.