Saudiyya na neman hauni

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Takobin haunin Saudiyya

Gwamnatin Saudiyya na neman masu bukatar yi mata aikin hauni, na aiwatar da hukuncin kisa da datse da hannu.

A sanarwar da gwamnatin ta fitar a shafinta na intanet ta bayyana ka'idojin daukar aikin, inda ta ce ba a bukatar masu sha'awar aikin su gabatar da shaidar karatunsu, sai dai akwai wasu sharudda takwas da ake bukatar su cimma bisa dokar gwamnati.

Ma'aikatar harkokin jama'a ta kasar ta ce, aikin haunin shi ne aiwatar da hukuncin kisa na fille kai da kuma datse hannayen masu laifi kamar yadda shari'ar musulunci ta tanada.

A Saudiyya dai aikin hauni shi ne fille kan masu laifi kamar wadanda suka kisan kai da masu fyade da masu fataucin miyagun kwayoyi da kuma datse hannayen barayi.