'Yan tawaye sun kwace sansanin sojin Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban mutane sun mutu a yakin Syria

Rahotanni daga Syria sun ce 'yan tawaye sun kwace iko da wani sansanin sojin gwamnati a lardin Idlib da ke arewa maso yammashin kasar.

Kungiyar sa ido kan kare hakkin bil adama a Syriar ta ce dakarun Syria sun janye daga sansanin Mastouma bayan wani kazamin fada tare mayakan 'yan tawaye.

Wannan ce dai nasara ta baya baya da yan tawayen suka samu a Idlib, wanda a halin yanzu suke iko da galibinsa.

'Yan tawayen sun hada da akasarin kungiyoyin masu tsatstsauran kishin Islama da suka hada da Jabhat al-Nusra mai alaka da Al-Qa'ida, wadanda a kwanan nan suka hadu suka kafa wata rundunar sojin da ake kira sojin nasara.