Amurka na tuhumar wasu 'yan kasar china

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da shugaba Xi na China Hakkin mallakar hoto xinhua
Image caption Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da shugaba Xi na China

Amurka ta tuhumi 'yan kasar China 6 da laifin leken asiri a fannin tattalin arziki, kuma 3 daga ciki sun kai matsayin Furofesa.

Ma'aikatar Shari'ar Amurka na zargin mutanen da satar sirri da fasahar da ake amfani da ita wajen hada wasu wayoyin salula.

Ta kuma ce suna mika bayanan da suke tattarawa ne ga wasu jami'o'i da kamfanonin da ke karkashin gwamnatin China.

Takardar tuhumar da ake masu na cewa an aikata laifin ne kusan shekaru goma da suka wuce.

Biyu daga cikin masu rike da mukamin Farfesan ne suka fara aikata laifin, lokacin suna aiki da wani kampanin Amurka mai yin wata manhaja da ke ba wayoyin salula da sauran na'urori damar taace signa ta sautin radio.

A farkon wannan wata ne aka kama daya daga cikinsu, Hao Zhang, lokacin da yake shiga Amurka.