"Zan karbi shawarwarin gudanar da mulki"

Image caption Muhammadu Buhari zai karbi shawarwari daga ciki da wajen Nigeria kan yadda zai tunkari matsalolin Nigeria

A ranar Laraba ne za'a fara taron kwanaki biyu na kwamitin da jam'iyar APC ta kafa domin tattaunawa kan tsara muhimman abubuwan da gwamnatin Muhammadu Buhari za ta maida hankali a kai wajen tafiyar da lamuran mulkin kasa.

Ana dai sa ran taron zai tantance shawarwarin da bangarori daban-daban na ciki da wajen kasar su ka bayar, wajen tafiyar da sabuwar gwamnati mai jiran gado a Najeriya.

Shugaban Najeriya mai jiran gado ya samu shawarwari da dama dangane da yadda zai gudanar da mulkin kasar.

Cikin wadanda za su halarci taron bayar da shawarwarin har da tsohon Firai Ministan Burtaniya Tony Blair.

Najeriya dai na fuskantar dimbin matsalolin da jama'ar kasar ke cewa lallai ya zama wajibi a kawo karshen su.