An dage zaben 'yan majalisa a Burundi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan Burundi na adawa da tazarcen Mr Nkurunziza

Shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza ya sanar da jinkirta ranar zaben 'yan majalisar dokoki zuwa karin kwanaki 10 masu zuwa.

A baya an shirya gudanar da zabukan ne a ranar Talata mai zuwa.

'Yan adawa da wasu shugabanni a shiyyar gabashin Afrika sun bukaci a jinkirta zaben domin tabbatar da cewa kura ta lafa kafin zaben.

An shafe makonni ana gudanar da zanga-zangar adawa da yunkurin tazarce na shugaba Nkurunziza.

A makon da ya gaba wasu manyan sojoji sun gamu da cikas a yunkurinsu na yi wa shugaban juyin mulki.