Wani mutumi ya yaudari 'yan matan 17 a China

Image caption Asirin Mr Yaun ya tonu a lokacin da matan suka je duba shi a asibiti

'Yan sanda sun damke wani mutum a China wanda ya yaudarar 'yan mata 17, bisa laifin yin zamba.

A watan da ya gabata mutumin, mazaunin lardin Hunan ya jawo hankali kafafan yada labarai da dama, a lokacin da matan 17 suka gano junansu yayinda suka je duba shi a asibiti.

A cewar wata jaridar China mai suna South China Morning, ana zargin shi da almundahana na wasu kudade da yake dauka a kai a kai daga matan da ya yaudara.

Jaridar ta ce matan sun kirkiri wata kungiya a shafin internet mai suna "Revenge Alliance" wato ramuwar gayya.

Jaridar ta kara da cewar, a kungiyar ta internet wacce suke tattaunawa suka gano cewa yana tamabayar 'yan matan kudi ko wani wata.

Rahotanni sun bayyana cewar, mutumin wanda ake kira Mr Yuan daga birnin Changsha, a lardin Hunan, daya daga cikin matan ta haifar masa kuma yana shirin aure da wata.

"Taro mara kintsi"

An gano cewar yana muamala da matan a lokaci daya, wasu har tsawon shekaru, a lokacin da likitoci ke neman 'yan uwan sa bayan da ya yi hatsari a watan da ya gabata.

Xiao Li wacce ta shafe watanni 18 ta na tare da shi, ta shaidawa wata jaridar china, Xiaoxiang Chen Bao cewar "Na damu sosai a lokacin da na ji cewar ya na kwance a asibiti."

"Sai dai kuma da na ga kyawawan mata suna ta tururuwar zuwa dubiya, sai na kasa kuka."

A lokacin da labarin ta ra 'yan matan da yake yi ya bazu, duban mutane sun fadi ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta na zamani game da karfin halin na Mr Yuan a inda wasu kuwa suka jinjinawa kokarinsa na tara 'yan mata.