Macky Sall ne sabon shugaban ECOWAS

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba MAcky Sall na Sinigal

Kungiyar Ecowas ta zabi shugaban kasar Sinigal Macky Sall a matsayin sabon shugaban kungiyar.

An zabi shugaba Sall ne a taron kungiyar karo na 47 ranar Talata a babban birnin Ghana, Accra.

Macky Sall ya gaji shugaban Ghana John Mahama Dramani wanda ya ja ragamar kungiyar har karo biyu.

A yayin taron dai wanda aka yi cikin kwanaki biyu, shugaba Mahama ya yi kira ga takwarorinsa shugabannin kasashen yankin Afrika ta yamma da su dauki matakin gaggawa wajen magance matsalar rashin aikin yi ga matasa a shiyyar.