Rikicin kabilanci ya barke a Ekiti

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sandan Najeriya cikin shirin ko ta kwana

Rahotanni daga garin sabuwar Ekiti da ke jihar Ekiti na kudancin Najeriya na cewa rikici ya barke mai nasaba da kabilanci da safiyar ranar Laraba.

Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa rikicin ya faro ne daga tashar mota da ke garin, wajen da ya zama matattarar Hausawa da Yarbawan.

Zuwa yanzu dai ba a tabbatar da ko akwai mace-mace ko adadin wadanda aka ji wa raunuka ba, amma rahotanni sun ce kwamishinan 'yan sanda jihar ya ce wurin domin shawo kan lamarin.

An sha fama da rikici mai nasaba da kabilanci a sassa daban-daban na Nigeria, lamarin da ka janyo hasarar rayuka da dukiyoyi.