Za a taimakawa dubban 'yan cirani

Hakkin mallakar hoto reuters
Image caption 'Yan cirani daga Afirka na cin bakar wahala wajen shiga Turai

Kasashen Malaysia da Indonesia sun amince da baiwa wasu 'yan cirani dubu bakwai mafaka, wadanda ke watangari akan kwale kwale a gabar tekun kasashen tare da karancin abinci da kuma ruwan sha

Bayan ganawarsu a Kuala Lampur tare kuma da kasar Thailand, kasashen sun dau alkawarin taimakawa 'yan ciranin matukar kasashen duniya zasu taimaka wajen sake tsugunar da su a wani wajen daban cikin shekara guda

Kasashen uku sun bayyana damuwarsu matuka game da jin dadin wadanda ke cikin jiragen ruwan, wadanda yawancinsu suka fito daga Myanmar da kuma Bangaladesh

A baya dai an soki kasashen Malaysian da Indonesia da Thailand saboda kafewar da sukayi cewa ba zasu karbi 'yanciranin ba