Shugaban PDP Adamu Mu'azu ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Adamu Muazu da su Shugaba Jonathan a lokacin kamfe

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Alhaji Ahmed Adamu Mu'azu ya murabus a matsayin shugaban jam'iyyar nan take.

Mataimakin kakakin jam'iyyar PDP, Barrister Abdullahi Jalo ne ya tabbatarwa da BBC murabus din Adamu Mu'azu a wata hira ta wayar tarho.

Tun bayan da jam'iyyar PDP ta sha kaye a zaben shugaban kasa a watan Maris, wasu jiga-jigan jam'iyyar ke ta yin kira ga Adamu Mu'azu ya sauka daga kujerar shugabancin jam'iyyar.

Daga cikin wadanda aka ambato suna kira ga Muazu ya sauka hadda gwamnan Jigawa, Sule Lamido da na Naija, Muazu Babangida Aliyu da kuma na Ekiti Ayo Fayose.

Jam'iyyar PDP ta shafe shekaru 16 ta na mulki a Nigeria, kafin Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ta samu galaba a kan Shugaba Goodluck Jonathan a zaben da aka yi a watan Maris.