Sojin Faransa sun yi arangama da masu fasa kwauri

Image caption Yadda masu fasa kwabri suke boye kamanninsu a Nijar

Sojojin Faransa sun ce sun kwato makamai da kuma miyagun kwayoyi bayan wata musayar wuta da suka yi da masu fasa kwabri a Jamhuriyar Nijar.

Rundunar sojin ta ce sojojin sun bude wutar ne bayan da wasu manyan motocin daukar kaya biyu suka haura shingen da aka sanya a kan titi da gudun tsiya.

A cikin motocin, sojojin sun ga tan daya da rabi na wiwi da tarin bindigogi da kuma wayoyi.

An dai halaka masu fasa kwabrin su uku, sannan an cafke uku daga cikinsu a lokacin da ake musayar wutar.

Faransan dai ta ce masu fasa kwabrin na da alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda.

Masu aiko da rahotanni sunce wannan shine aikin kwace miyagun kwayoyi mafi girma da aka gudanar, tun lokacin da Faransan ta soma kaddamar da farmaki a kan masu tsatsauraran ra'ayin addini a Nijar da kuma wasu bangarori na yankin sahel a shekarar 2013.