Mayakan IS sun kame birnin Palmyra

Wuraren tarihi a Palmyra
Image caption Wuraren tarihi a Palmyra

Rahotanni na cewa Mayakan IS a kasar Syria sun kame birnin Palmyra, wanda ke cike da wuraren tarihi a Gabas-ta-tsakiya.

Ana dai fargabar cewa mayakan za su lalata wuraren tarihin da ke birnin idan suka kammala kama shi.

Wuraren tarihin na duniya na sashen kudancin sabon birnin ne.

Shugaban hukumar kula da kayan tarihi na Syria ya ce an kwashe daruruwan kayan tarihi masu muhimmanci ya zuwa wani amintaccen wuri daga gidan tarihin.