APC ta kai gwamnan Kaduna gaban EFCC

Image caption Zababben gwamnan Kaduna Nasir Elrufai

Zababben gwamnan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, Malam Nasiru El Rufa'i, ya aika da takardar koke ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, game da wani yunkuri na gwamnatin jihar mai barin gado na kashe wasu kudade.

Sabon zababben gwamnan ya bukaci hukumar EFCC ta binciki yunkurin gwamnatin na neman rarraba kudaden rarar man fetur sama da Naira biliyan biyu yayin da ya rage kwanaki kadan su mika mulki.

Kwamitin karbar mulki na sabon gwamnan ya ce sun rubuta wa kungiyar kwadago ta NLC a jihar da ta ma'aikatan kananan hukumomi NULGE a game da yunkurin.

Kwamitin ya yi gargadin cewa duk jami'in da ya bari aka yi amfani da shi wajen kashe kudin zai gamu da hukunci idan gwamnati mai jiran gado ta kama aiki.

Sai dai wani babban jami'i a gwamnatin mai barin gado ya ce har yanzu, wa'adin gwamnati mai ci bai kare ba, saboda haka tana da ikon kashe kudin gwamnati wurin gudanar da ayyuka.