'Yan al-Shabbab sun gargadi Musulman Kenya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan Al-Shaabab da ke Somaliya na yawan kai hare-hare a Kenya

Shugabannin al'umma a Kenya sun ce mayakan sa kai na kungiyar al-Shabbab sun karbi ikon wani masallaci na dan lokaci a garin Garissa.

Rahotanni sun ce masu da'awar jihadin sun yi wa mutanen da suka samu a cikin masallacin jawabi na tsawon sa'o'i biyu kafin daga bisani suka shige daji suka tafi.

A cikin jawabin da su ka yi wa jama'a, masu da'awar jihadin sun gargadi mutane kan yi wa hukumomin gwamnati leken asiri.

A watan da ya gabata ne 'yan al-Shabbab suka yi wa wata jami'a a garin Garissa kawanya, inda suka kashe kimanin mutane 150.

Cibiyar kungiyar dai a Somaliya take amma kuma ta na tasiri ma a Kenya.