Malaysia ta ba da umurnin ceto 'yan ci rani

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu tafiya ci rani ta jiragen ruwa

Firai ministan Malaysia Najib Razak, ya ce ya umurci sojojin ruwa da sauran hukumomin sufurin ruwa na kasarsa da su yi kokarin gano 'yan ci ranin da suka makale a teku domin ceton su.

A 'yan kwanaki da suka gabata, Malaysia ta kasance tana hana jiragen ruwa masu dauke da 'yan ci rani tsayawa a gabobin tekunta.

'Yan ci ranin sun hada da 'yan Bangaladash da kuma Musulman Rohingya da suke gujewa gallazawar da suke fuskanta a Myanmar.

Mista Razak ya ce Malaysia tana da alhakin kiyaye mutuwar mutanen.

A wani labari kuma, Australia tace ba za a kyale 'yan gudun hijira 'yan Kabilar Rohingya wadanda suka isa kasar ta jirgin ruwa su shiga cikin kasar ba.

Firai Ministan Kasar Tony Abbot ya ce yana da muhimmanci a hana fataucin bil adama.