Myanmar za ta shiga tattaunawa kan 'yan ci-rani

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Malaysia ta ce za ta dauki 'yan ci-ranin

Mahukunta a Myanmar sun ce za su halarci wani taron gaggawa da za a yi a Thailand a mako mai zuwa don duba hanyar maganace matsalar 'yan gudun-hijira ko ci-rani a yankin.

Ana dai kokwanto game da halartar tasu, duk kuwa da matsin-lambar da kasashen duniya ke musu.

Galibin dubban 'yan gudun-hijirar da suka makale a teku, Musulmi ne Rohingya , wadanda suka tsere daga Myanmar, inda aka ki amincewa da su a matsayin 'yan kasa.

Ministocin harkokin wajen Indonesiya da Malaysia da wasu jami'an Amurka a yanzu haka suna can a Myanmar domin tattauna batun.

Tunda farko, Firai ministan Malaysia Najib Razak, ya ce ya umurci sojojin ruwa da sauran hukumomin sufurin ruwa na kasarsa da su yi kokarin gano 'yan ci ranin da suka makale a teku domin ceton su.

A 'yan kwanaki da suka gabata, Malaysia ta kasance tana hana jiragen ruwa masu dauke da 'yan ci rani tsayawa a gabobin tekunta.