Buhari: Kiristoci za su yi azumin kwanaki uku

Hakkin mallakar hoto apc
Image caption A ranar 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da Muhammadu Buhari

A yayin da ya rage 'yan kwanaki a rantsar da sabuwar gwamnati a Najeriya, wata kungiyar Kiristocin arewacin kasar na shirin fara wani azumi da gudanar da adduoi na musamman.

Kungiyar Kirstocin za su yi azumin ne domin ganin sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta sami nasara a gudanar da mulkin kasar.

Kungiyar ta mabiya addinin kirista a arewacin Najeriya mai suna Christian Eagle eye, ta ce azumin da adduo'in nasu, na cikin gudunmawar da za su bai wa gwamnatin Buhari.

Ranar 28 da 29 da 30 ga wata ne dai, 'ya'yan Kungiyar suka ce za su gudanar a azumin.