Ba ma tare da masu batanci ga Annabi - Dahiru Bauchi

Image caption A taron Maulidin Nyass mutumin ya yi kalaman

Manyan shehunnan darikar Tijjaniyya a Nigeria sun nisanta kansu da wasu kalaman rashin girmamawa da wani ya yi a kan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallama a Kano cikin makon da ya gabata.

Kalaman wadanda aka yi su a wajen wani Maulidin Shehu Ibrahim Inyass, sun tayar da hankulan jama'a da dama a kasar.

Shahararren malamin darikar Tijjaniya a Nigeria, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce duk wanda ba ya girmama Annabi, ba ya tare da su kuma tuni suka kai kara wajen 'yan sanda domin a hukunta mutumin.

"Duk wanda ba ya ganin girman Manzon Allah ba ya tare da mu. Ba ruwanmu da shi, wadannan mutanen kuma ba 'yan Tijjaniyya bane," in ji Sheikh Dahiru Bauchi.

Ya kara da cewar "Mun dauki mataki mun ce duk inda aka ga irin wadannan mutanen, a hada su da 'yan sanda, domin su ba 'yan Tijjaniya bane, su na bata mana suna."