Nkurunziza yana murza leda a Bujumbura

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shagaban Burundi yana buga kwallo a lokacin da mutane ke zanga-zanga

An dauki hoton shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza yana murza leda a filin wasa, duk da zanga-zangar da ake yi kan batun ci gaba da shugabancinsa karo na uku.

Mr Nkurunziza ya kan yi atisaye a kowacce rana tare da abokansa a babban birnin kasar Bujumbura.

A wata sabuwar zanga-zanga da aka yi an harbe mutum guda a Bujumbura.

Makon da ya gabata ne aka yi yunkurin juyin mulki a kasar wanda ba a yi nasara ba, inda aka zargi manyan jami'an tsaro da sojoji kan juyin mulkin.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Nkurunziza kwararen kocin kwallon kafa ne
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption A cewar sa ya iya zura kwallo

A ranar Laraba, Mr Nkurunziza ya bukaci 'yan kasar da suka tserewa tsoron rikici a kasar da su dawo a ci gaba da zama, inda ya ce ana zaune lafiya da juna.

Hukumar 'yan gudun hijira ta majalissar dinki duniya ta ce sama da mutane 105,000 ne suka fice daga Burundi zuwa makwabtanta tun lokacin da aka fara yamutsin.

Mr Nkurunziza ya sanar da jinkirta zaben majalisar dokoki na tsawon kwanaki 10.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban kasar na da kungiyar kwallon kafa da ake kira Hallelujah FC
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ya kware a murza leda

Ya ce ya yanke shawarar ce bayan da hukumar zaben ta bukaci a yi hakan, in ji kakakinsa.

Kungiyar Tarayyar Afrika- AU da ta EU sun yi kira a dage zaben domin a ci gaba da tattaunawa har sai kura ta lafa.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An san Mr Nkurunziza da jarabar son kwallo

Masu sukar Mr Nkurunziza sun ce wa'adin mulki na uku, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa, a don haka gwamma ya sauka.

Za a gudanar da zaben shugaban kasa a watan Yuni.