Obama: Kwace Palmyra babbar koma baya ce

Hakkin mallakar hoto Unknown

Obama yace baya tunanin mayakan sun yi galaba akan sojojin gwamantocin Amurka da Iraqi.

A cikin wata hira da yayi da wata mujalla, Mr Obama ya yi alkawarin kara bayar da taimako ga dakarun Iraqi inda yace Amurka zata kara horar da sojojin dake a yankunan 'yan sunni.

A bangare guda kuma Rasha ita ma ta ce za ta samar da karin makamai ga Iraqi.