Amnesty ta ja kunnen Qatar a kan 'yan ci rani

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An zargi Qatar sa cin zarafin 'yan ci rani dake aikin leburanci a kasar

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnnesty International ta ce dole ne Qatar ta inganta yanayin da 'yan ci rani da ke aiki a kasar ke ciki, yayin da take shirin karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafar duniya a shekarar 2022.

Amnesty tace gwamnatin Qatar ta samu nasara 'yar kadan a kan alkawuran da tayi a bara, kuma har yanzu ma'aikata na bukatar izinin wadanda suke yiwa aiki kafin su canza ayyukansu, ko su bar kasar.

Ta ce ana samun tafiyar hawainiya sosai wajen aiwatar da sauyi mafi mahimmanci, wato yanayin yadda ake biyan ma'aikatan.

Ministan Kwadagon Qatar ya ce yana da tabbacin cewa za a aiwatar da sauye-sauye a dokokin daukar ma'aikata zuwa karshen shekara.