Shan Paracetamol na iya cutar da jariri a ciki

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mace mai ciki

Masana kimiyya a Biritaniya sun ce wani bincike da suka yi a kan maganin kashe radadi da aka fi sani da Paracetamol ya nuna cewar maganin na iya cutar da jaririn da ke cikin mahaifiyarsa, musamman ga masu cikin da suka yi amfani dashi na tsawon lokaci.

Masana kimiyyar na jam'iar Edinburgh da ke Scotland sun yi gwajin a kan beraye ne, inda suka sanya musu wani bangare na dan tayi wanda zai zama tamkar suna da juna biyu, kuma sai suka gano cewar berayen, wadanda aka bai wa magananin kashe radadi wato Paracetamol na tsawon kwanaki bakwai sun samu raguwar wata kwayar halitta da ake samu a jikin 'ya'ya maza watau "testosterone".

Kwayar halittar, tana da muhimmanci wajen bunkasa halittar 'ya'ya maza wajen samun haihuwa a rayuwarsu.

Hukumar lafiya ta Biritaniya ta ce kada mata masu ciki su sha maganin har sai ya zama dole, kuma idan har ya zama dolen to su sha na gajeran lokaci.