"Gwamnatin APC za ta dade bata kai gacci ba"

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Shugaba mai jiran gado da shugaba mai barin gado

A ranar Alhamis ne aka kammala wani taro na kwanaki biyu na kwamitin da jam'iyyar APC ta kafa domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan yadda za ta aiwatar da muhimman abubuwan da gwamnatin Muhammadu Buhari za ta maida hankali a kai, wajen tafiyar da lamurran mulkin kasar.

Mahalarta taron daga ciki da wajen kasar sun bayar da shawarwari kan al'amura da dama, da suka hada da hanyoyin da za a warware matsalolin da suka dabaibaye tattalin arzikin kasar da tabarbarewar tsaro da kuma uwa-uba cin hanci da rashawa da Najeriyar ta yi kaurin suna a kansa.

To sai dai kuma masana da dama da suka bayar da shawarwari a taron, sun ce saboda tabarbarewar al'amurra, za a dauki lokaci kafin sabuwar gwamnatin ta APC ta cimma manufofin ta.

Tsohon babban hafsan hafsoshin sojin Najeriya Laftanal Janar Abdurrahman Dambazau ya shaida wa BBC cewa "Farfado da sha'anin tsaro zai dauki lokaci mai tsawo saboda ya kunshi abubuwa da dama da suka hada da rashin ayyukan yi, amma muna da yakinin cewa gwamnatin Buhari za ta kawo sauyi."

A ranar 29 ga watan Mayu ne gwamnatin APC karkashin jagorancin Janar Muhammadu Buhari za ta karbi ragamar mulkin Najeriya daga hannun Goodluck Jonathan na PDP.