An kona tsohuwa bisa zargin maita a Kebbi

Hakkin mallakar hoto bb
Image caption 'Yan sanda na bincike kan wadanda suka kona tsohuwa a Kebbi

Rundunar 'yan sanda a Jihar Kebbi na bincike kan yadda wasu gungun mutane a garin Argungu suka kona wata dattijuwa har lahira bisa zarginta da maita.

Mutanen suna zargin matar da fakewa da bara gida-gida wajen kama kurwar jama'a.

Kwamishinan 'yan sanda na Jihar Kebbi Mr Danladi Mshelbwala, ya tabbatar wa da BBC aukuwar lamarin.

"Mun sami labarin afkuwar wannan lamari amma koda mutanenmu suka je wajen sai konanniyar gawar tsohuwar suka samu," in ji Mr Mshelbwala.

Ya kuma ce rundunar 'yan sandar jihar za ta dauki mataki kamar yadda doka ta tanadar.