Bom ya halaka jama`a a Burundi

Hakkin mallakar hoto

Wani harin bam da aka kai a tsakiyar Bujumbura babban birnin kasar Burundi ya yi sanadin mutuwar mutum biyu, yayin da wasu da dama kuma suka samu raunuka.

An kai harin ne lokacin da ake cigaba da zanga-zangar kin matakin ta-zarcen da shugaba Pierre Nkurunziza ya dauka na neman wa'adin mulkin kasar a karo na uku.

Tun da farko Majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa ana samun karuwar masu kamuwa da cutar amai da gudawa a tsakanin 'yan gudun hijirar kasar da suka gudu Tanzania sakamakon rikicin siyasar kasar.

Majalisar ta ce kusan mutum dubu ne suka kamu da cutar.

Mai magana da yawun hukumar dake kula da 'yan gudun-hijra na majalisar dinkin duniya Adrian Edwards ya bayyana cewa har yanzu 'yan gudun hijira na cigaba da yin tururuwa daga Burundi zuwa makwabtan kasar.

Ya zuwa yanzu dai mutum 31 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar amai da gudawa.