Mayakan IS na nausawa cikin birnin Baghdad

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Mayakan IS a Syria a Iraqi na samun galaba akan kawancen sojojin da Amurka ke jagoranta

Akwai rahotannin da ke cewa mayakan IS wadanda suka kwace birnin Ramadi na Iraqi a ranar Lahadi, a yanzu su na nausawa zuwa Bagadaza babban birnin kasar.

Wannan dannawar da suke ta baya bayan nan, na zuwa ne baya da mayakan IS suka kwace ikon birnin Palmera na Syria daga dakarun da ke goyan bayan gwamnati dama mashigar iyaka ta karshe da ta rage a hannun Gwamati.

Shugaba Obama dai ya amince cewa an samu koma baya a yakin da ake da mayakan IS.

Amma ya hakikance cewa ba wai ana samun rashin nasara bane a kan mayakan.