Boko Haram: Jama'a na cikin mawuyacin hali

Image caption Jama'a sun ga abubuwa na tashin hankali da firgici sakamakon hare haren Boko Haram

Shugaban kwamitin bayar da agaji na Red Cross ya bayyana halin da jama'a suke ciki a arewa maso gabashin Nigeria, inda mayakan Boko Haram suke tayar da kayar-baya a matsayin daya daga cikin mafi muni a duniya

Bayan da ya ziyarci yankin, Peter Maurer ya ce mai yiwuwa mutane a yankin za su kasance ne cikin damuwa na lokaci mai tsawo, dangane da irin abubuwa na tashe- tashen hankula da suka gani.

Mutane kimanin miliyan daya da rabi ne suka rasa matsugunansu a 'yan shekarun nan.

Red Cross na daya daga cikin kungiyoyi 'yan kalilan dake aiki a yankin.

Ta kuma mika kokon bararta, na neman dala miliyan 65 domin gudanar da aikace-aikacenta a kasahen da wannan tashin hankali ya shafa, da suka hada da Najeriya da Chadi da Kamaru da kuma Nijar.