An killace 'yan hijirar Malkohi a cibiyar soji

Image caption Wasu 'yan gudun hijira a Najeriya

A Najeriya, ana ci gaba da samun karin bayanai dangane da inda ake ajiye wasu mata da kananan yaran nan da aka ceto daga dajin Sambisa, wadanda sojoji suka kwashe daga sansanin 'yan gudun hijira na Malkohi da ke jihar Adamawa.

Bayanan da BBC ta samu sun tabbatar da cewa mutanen su kimanin 260 an ajiye su ne a wani wuri mallakin sojin kasar, inda ake ci gaba da bincike a kansu, da taimaka musu dawowa cikin hayyacin su.

Kwashe matan da yaran daga farko ya haifar da damuwa a game da makomar su, musamman ma ganin yadda a farko babu wani daga cikin mutanen gari da yasan inda aka kai su da aka kwashe su daga sansanin 'yan gudun hijirar.

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa BBC cewa matan da yaran suna wani wuri mallakin soji cikin kwanciyar hankali, inda ake yi musu magani kafin a tantancesu.

Gwamnatin ta nuna damuwa bisa yadda, mai yiwuwa wasu daga cikin matan sun dauki tsattsaurar akidar Boko Haram lokacin da a ke tsare da su, kuma ana gudun kada su yada akidar idan sun koma garuruwansu.

BBC ta fahimci cewa wannan ya na daga cikin dalilan da suka sa a ka kwashe matan zuwa ma'aikatar soji.