An kai hari a Masallacin 'yan Shi'a a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Shi'a na zargin ana gallaza musu a Saudiyya

Rahotanni da ke fitowa daga Saudiyya na cewa an kai harin kunar bakin wake kan wani masallacin mabiya Shi'a a yayin da ake sallar Juma'a.

Rahotanni sun ce mutane da dama sun samu raunuka sakamakon harin wanda ya faru a wani kauye da ke lardin gabashin kasar, inda mabiya Shi'a ke zaune.

Wani da aka yi abin a idonsa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa kusan mutane 30 ne suka ji rauni a harin da aka kai a Masallacin da ake kira Imam Ali.

Mabiya Shi'a da ke yankin dai sun sha yin zanga-zanga domin neman karin 'yanci.

Wannan harin dai shi ne irinsa na farko da aka kai wa mabiya Shi'a a yankin, kuma hakan na zuwa ne yayin da Saudiyya ke jagorantar rundunar hadin gwiwar sojin kasashen larabawa da ke kai hare-hare a kan mabiya Shi'a da ke Yaman.