Buhari ya gana da shugaban Burtaniya

Firaministan Burtaniya David Cameron ya tattauna da shugaba mai jiran-gado na Najeriya Muhammadu Buhari ranar Asabar a London.

Sun tattauna ne a fadar gwamnatin Burtaniyar akan matsalar Boko Haram da sauran harkokin tsaro da na tattalin arziki.

Wani kakakin fadar gwamnatin Burtaniya ya ce Burtaniyar ta yi alkawalin tallafa wa Najeriya wajen yakar Boko Haram, da miyagun laifuka da kuma matsalar cin hanci na rashawa.

Ta kuma nemi taimakon Najeriya wajen tinkarar matsalar kwararowar 'yan ci-rani daga Afrika zuwa Turai.

Muhammadu Buhari ya basu tabbacin kare kan iyakokin Najeriya da yaki da cin hanci da rashawa.

Karin bayani