Sojin Iraqi sun kaddamar da hari kan IS

Hakkin mallakar hoto Reuters

Sojojin Iraqi sun yi luguden wuta akan mayaka masu da'awar kafa kasar musulunci a yankin Ramadi, a karon farko tun bayan da birnin ya fada hannun 'yan tawayen a makon da ya wuce.

Jami'ai sun ce sojoji da mayakan sa kai na shi'a sun fatattaki 'yan tawayen daga garin Hussaiba dake gabashin Ramadi.

A waje guda kuma mukaddashin jami'in hukumar taimakon agaji ta Majalisar Dinkin Duniya Dominik Bartsch ya baiyana damuwa akan halin da mutanen da suka tsere daga Ramadi suke ciki a gabar wata gada dake hanyar shiga Bagadaza.

" Yace muna sane da mutane kusan 40,000 wadanda suka bar Ramadi suke neman tsira daga fadan da ake fafatawa.

Yace hukumomi sun hana galibin mutanen shiga Bagadaza, yana mai cewa sun damu kwarai da halin da mutanen suke ciki musamman mata da yara kanana da kuma tsofafi