Buhari:Shugabanni 54 za su zo rantsarwa

Kerry da Muhari Hakkin mallakar hoto Buhari Campaign
Image caption Ana sa rai Sakataren kula da harkokin kasashen waje na Amurka John Kerry, zai jagoranci tawagar kasar zuwa bikin rantsar da Buhari a karshen watan nan

Sama da kimanin shugabannin kasashe 54 ne ake sa rai za su halarci bikin rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban kasa.

A jawabin da yayi wa 'yan jarida a Abuja, Mista Edem Duke Ministan al'adu da yawon bude ido, kuma shugaban karamin kwamitin yada labarai da tsare-tsaren shirin rantsar da shugaban kasar, yace yawancin wadanda suka nuna sha'awar halartar bikin daga kasashen turai ne.

Sannan ya kara da cewa 'mun dauki matakan tsaurara tsaro don ganin an gudanar da bikin lafiya'. Za kuma a rufe wasu hanyoyi a cikin Abuja musamman wadanda ke zuwa dandalin Eagle square. Sannan za'a yi binciken kwakwaf ga duk wadanda aka gayyata kafin su shiga wurin bikin'.

Za a gudanar da bikin rantsar da shugaba mai jiran gado Muhammadu Buhari a dandalin Eagle square ne a Abuja, ranar 29 ga wannan watan wanda kuma ranar hutu ce a duk fadin kasar a matsayin ranar dimukuradiyya.