Najeriya: Ministoci za su bayyana a gaban majalisa

Layin mai
Image caption Matsalar rashin mai ya haifar da dogayen layukan motoci a gidajen mai a Najeria

Kwamitin hadin gwiwa a kan man fetur da albarkatu kasa sun bukaci ministan kudi da tattalin arziki Dr. Ngozi Okonjo Iweala da ministan Mai Diezani Allison Madueke da su bayyana a gabanta a ranar litinin domin su yi bayyanin dalilin da yasa wahalar mai ya ki ci, ya ki cinyewa a kasar.

Cikin wadanda aka gayyata har da shugaban gungun kamfanonin man fetur na Najeriya NNPC Joseph Dawah da shugaban hukumar sa ido da kuma kayyade farashin man fetur da dangoginsa PPRC da kuma shugaban hukumar kula da albarakatun man fetur DPR

Karin wadanda kwamitin ya bukaci su bayyana a gabansa sun hada da wakilan kungiyoyin dillalan man fetur na Najeriya da kuma kungiyar masu motacin sufuri na

A sanarwar da shugabannin kwamitocin kula da hakar man fetur da kuma samar da shi, Sanata Emmanuel Paulker da Sanata Magnus Abe, sun ce wannan gayyata cika ummarnin majalisar dattijai ne a zamanta na ranar alhamis a inda ta bukaci kwamitocin su gayyacesu domin su yi bayanin dalilin da yasa ake fama da fama da rashin mai a kasar, domin a yiwa tufka hanci.