Ciwon zuciya na da alaka da bacin rai

Ciwon zuciya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ciwon zuciya

Dole ne a binciki masu fama da ciwon zuciya sosai domin a gano ko ciwon yana da alaka da wani bacin rai da suke fama da shi, kuma a rinka ba su shawarwari a cewar masana.

Sakamakon wani karamin bincike da aka gabatar ma kungiyar masana ciwace-ciwacen zuciya na Tarayyar Turai ya nuna cewa masu fama da wani bacin rai suna iya mutuwa a cikin shekara guda.

Kodayake dalilai da dama suna iya haddasa ciwon tare da kara zafafa shi, masu binciken sun ce yana da muhimmanci a yi kokarin yaye ma majiyyata ciwon bakin ciken dake damun su.

Kungiyoyin agaji sun ba da shawara ga mutane su rinka neman taimako daga kwararru ma'aikatan jiyya da likitoci.

Farfesa John Cleland babban mai bincike a wannan nazari da aka gudanar wanda ke aiki a duka Kolejin Imperial ta London da Jami'ar Hull ya bayyana ciwon zuciya a matsayin wata annoba da ta shafi mutane 900,000 a fadin Brittaniya.

To amma duk da kokarin nemo magungunan da suka dace da inganta hanyoyin neman magungunan, babu wani magani kamar yadda Farfesa Cleland ya shaida ma BBC.

Yace, "kasancewar mu, masana ciwace-ciwacen zuciya, mun maida hankali a kan kokarin nemo magunguna da hanyoyi da tiyata."

Ya kara da cewa, "suna aiki, amma kuma, ba yadda muke so ba. Don haka muka yanke shawarar komawa gefe daya, mu duba lamarin baki-dayansa."

Bugun zuciya na faruwa ne idan jijiyoyin zuciya suka yi rauni ko kuma suka yi tsauri, abinda zai hana su harba jini ga sauran sassan jiki.

A yayinda haka ta kasance, masu fama da ciwon kan yi laushi, wannan kuma zai iya kai su ga mutuwa.

A matsayin wani bangare na binciken da ake cigaba da yi, tawagar Farfesa Cleland, ta yi tambayoyi ga majiyyata 96 wadanda aka kwantas asibiti da ciwon zuciya domin tantance ko suna fama da wani bacin rai.

Karin bayani