An gano kaburburan 'yan ci rani a Malaysia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin cewa 'yan ciranin sun mutu ne a hannun masu garkuwa da su

'Yan sanda a kasar Malaysia sun ce sun samu kimanin kaburra 140 a wani daji mai iyaka da kasar Thailand.

Shugaban 'yan sandan kasar Khalid Abu Bakr, ya ce sun yi imanin cewa an binne 'yan ci ranin ne a cikin kaburburan bayan sun mutu a hannun masu tsare da su.

Dubban 'yan ci rani ne daga wurare daban-daban suke ketara tekun Andaman zuwa kasar Malysia domin neman na sawa a baka. Kuma ana zargin cewa wasu na garkuwa da su domin neman kudi.

Kasar Thailand dai tana yaki da batun fataucin 'yan ci rani kuma an yi yakinin cewa shirin da take yi ya bar dubban 'yan ci ranin cikin halin ni 'ya su, a cikin jiragen ruwa, a tekun Andaman.