An yi jana'izar 'yan Shi'a a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An yi jana'izar 'yan Shia a Saudiyya

Dubban 'yan Shia sun halarci jana'izar wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai wani masallaci a Saudiyya.

Mutane 21 ne suka rasa rayukansu a harin da aka kai ranar Juma'a a wani kauye da ke Qatif a gabashin kasar.

Mabiya sunni wadanda suke da alaka da kungiyar IS ne suka kai harin.

An tsauarara matakan tsaro saboda ana fargabar cewar kungiyar zata iya kai hari inda ake jana'izar.

Amma kuma anyi taron cikin kwanciyar hankali inda masu alhini suka mamaye titunan kauyen a lokacin da ako dauko gawarwakin zuwa makabarta.