Fada ya rincabe a Yemen

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Ana gwabza fada a Yaman

Rahotanni daga kudancin birnin Dalea na kasar Yaman sun ce ana gwabza kazamin fada a kasar inda 'yan bindiga suka fatattaki mayakan Houthi daga wani tsauni.

Amma kuma a birnin Taiz, mayakan sun fi karfin abokan adawa sakamakon fada da ake gwabzawa a kan titi.

Rundunar kawancen sojin da Saudiyya ke jagoranta sun ci gaba da kai harin sama a kan 'yan Houthi a Sanaa, babban birnin kasar da kuma wasu wuraren.

Rahotanni da ba'a tabbatar ba suna cewa an dage wata tattaunawar zaman lafiya da majalisar dinkin duniya ta shirya a yayin da ake ci gaba da fada.