An hallaka mutane fiye da 20 Benue

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin kabilanci na neman ya gagari kundila a Nigeria

An kashe mutane fiye da 20 sakamakon tashin hankali a wasu kyauyuka a jihar Benue da ke arewacin Nigeria.

Bayanai sun ce 'yan bindigar da ake zargin Fulani ne, sun kaddamar da hare-haren ne a wasu kyauka da ke karamar hukumar Logo ta jihar.

Kakakin 'yan sandan jihar, Austin Ezeani ya shaida wa BBC cewa "Wasu da ake zargin Fulani ne suka kaddamar da hari a kyauyukan uku na karamar hukumar Logo inda suka hallaka mutane 23."

Rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma a wasu sassan Nigeria ya janyo mutuwar mutane da dama da hasarar dukiya a cikin 'yan shekarun nan.

Tashin hankali mai nasaba da kabilanci ya fi muni ne a jihohin Benue da Taraba da Kaduna da kuma Filato.