NDLEA na shirin mika Kashamu ga Amurka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kashamu ya musanta zargin da ake masa

Hukumomi a Najeriya na kokarin mika zababben Sanata Buruji Kashamu a gaban wata kotu a Amurka inda ake neman sa ruwa a jallo kan zargin safarar miyagun kwayoyi tun shekaru 20 da suka wuce.

Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta Najeriya, watau NDLEA ta tsare da Buruji Kashamu a gidansa tun makon baya.

A ranar Litinin ya ki bayyana kan sa a gaban kotu.

Buruji Kashamu ya karyata zargin, ya ce jami'an Amurkan sun yi kuskure ne, kaninsa da ya rasu suke nema ba shi ba.

Al'amarin dai har ya janyo hankalin tashoshin telabijan din Amurka, kuma suna shirin tsara wani shiri yau da kullum da suka yi wa lakabi da, ja ko baki?