Mutane billiyan 3.2 ke amfani da Intanet

Masu amfani da internet Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu amfani da internet

Kimanin rabi na al'ummar duniya ne wani sabon rahoto ya bayyana cewar za su yi amfani da hanyar sadarwa ta zamani internet zuwa karshen wannan shekarar.

Kungiyar sadarwa ta duniya ITU wani reshe na Majalisar Dunkin Duniya ya yi hasashen cewar sama da mutane billiyan 3 za su rinka amfani da wannan hanya.

An yi kiyasin yawan al'ummar duniya a yanzu a kan billiyan 7 da digo biyu.

Rahoton ya kara da cewar kimanin billiyan biyu ne za a samu daga kasashe masu tasowa.

To amma kusan miliyan 89 za a same su ne a kasashe irinsu Somalia da Nepal.

Wadannan dai suna cikin jerin kasashen da Majalisar Dunkin Duniya ke ganin cigaban su bai kai ya komo ba, kuma dadinsu bai wuce miliyan 940 ba.

Hukumar ta ITU tace, za a kuma samu sama da hanyoyin sadarwa na tafi-da-gidan billiyan 7.

Hukumar ta gano cewar cikin mutane 100 za a samu 78 a kasashen Amurka da Turai dake amfani da hanyar sadarwa mai sauri ta zamani, kashi 69 cikin dari kuma na amfani da matsakaiciyar hanyar - kashi 29 ne kawai cikin dari ake wadatarwa da hanyoyin a yankunan karkara.

Afrika ce dai koma-baya, inda kashi 17 da digo 4 ke amfani da hanyar sadarwar mai sauri ta zamani.

Rahoton ya cigaba da cewa zuwa karshen shekara, kashi 80 cikin dari na gidaje a kasashen da suka cigaba da kuma kashi 34 cikin dari a kasashe masu tasowa za su iya yin amfani da hanyar sadarwar ta zamani watau internet.

Rahoton ya maida hankali ne kan nazarin cigaban da aka samu na amfani da hanyar sadarwa ta zamani cikin shekaru goma sha-biyar da suka wuce.

Karin bayani