Kenya: 'Yan sanda sun yi arangama da 'yan Al-Shabab

Image caption 'Yan sandan kasar Kenya

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Kenya ta tabbatar da cewa dan sanda daya ne kawai ya samu raunuka sakamakon arangamar da 'yan sanda suka yi da mayakan Al-Shabab a kauyen Yumbis da ke Garissa, a arewa maso gabashin kasar.

Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida Mwenda Njoka, ya shaida wa BBC cewa an yi mummunar musayar wuta tsakanin 'yan sandan da mayakan na Al-Shabab.

Rahotanni da suka fito daga farko sun nuna cewa an kashe 'yan sanda da dama a harin wanda aka kai ranar Litinin da daddare.

Kazalika kungiyar Al-shabaab ta fitar da wata sanarwa inda ta dauki alhakin kai harin.

Kakakin kungiyar ya yi ikirarin cewa sun kashe 'yan sanda 20, amma ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta ce hakan wata farfaganda ce kawai.